An nada shugaban riko na nukumar tsaro sirri ta DSS


A fadar shugaban kasa a ranar Talata ta tabbatar da nadin, Matthew Seiyefa, a matsayin shugaban riko na hukumar tsaron sirri ta DSS.

Kafin nadin nasa Seiyefa ya kasance jami’i mafi girman mukami a hukumar idan ka ɗauke tsohon shugabanta Lawal Musa Daura.

Sanarwar nadin nasa na kunshe ne cikin wani sako da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin Najeriya.

Tun farko mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shine ya cire shugaban hukumar ta DSS bayan da jami’an hukumar suka hana yan majalisun tarayya shiga harabar majalisar.

Seiyefa zai cigaba da rike mukamin a matsayin shugaban riko.


Like it? Share with your friends!

-1
68 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like