An Maka Rarara A Kotu Bisa Zargin Sanya Matar Aure A Bidiyon Wakarsa


A karshe dai hukumar kare hakkin bil Adama reshen jihar Kano ta maka mawaki Dauda Kahutu Rarara a kotu bisa ikrarin da wani miji ya yi na cewar Mawakin ya yi amfani da matarsa a bidiyon wakarsa ta ‘Jahata ce’. An kai karar mawakin ne Kotun Kofar Kudu dake daura da masarautar Kano.

Shi dai Abdulkadir Inuwa Indabawa yana zargin Rarara da boye masa mata tare da amfani da ita cikin bidiyonsa na wakar Jahata ce a matsayin Jarumar wakar ba kuma tare da saninsa ko amincewarsa ba.

Tun a farkon lamarin ne hukumar ta kare hakkin bil’adama ta aikewa mawakin sammaci tana neman da ya gurfana a gabanta don jin bahasin korafin da aka yi a kansa, sammacin da mawakin yayi watsi da shi.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like