An lalata kwalaben giya sama da miliyan ɗaya a Kano


Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben giya guda miliyan 1,975,000 da kudinsu ya kai sama da naira miliyan 200.

Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa,Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ta’ammali da giya da kuma amfani da kayan da suke saka maye abu ne da yake haramun a shariar musulunci.

Gawuna ya ce tuni gwamnatin jiharta shirya tsaf domin yi wa ma’aikaci Hisbah karin albashi a wani kokari na kara musu kaimi kan namijn kokarin da suke yi.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 11

Your email address will not be published.

You may also like