An lalata allunan yakin neman zaben Yahaya Bello


An lalata wasu daga cikin allunan yakin neman zaben, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da aka saka a wasu wurare dake Lokoja babban birnin jihar.

A wani fefan bidiyo da babu kwanan watan da aka dauke shi ya nuna yadda wasu mutane suke lalata allunan dake dauke da hoton Yahaya Bello da kuma mataimakinsa Edward Onoja.

Itama yar takarar jam’iyar SDP Natasha Akpoti ta zargi gwamna Yahaya Bello da tura yan daba su lalata mata ofishin yakin neman zabenta.

An shirya zaben gwamnan jihar Kogi zai gudana ranar 16 ga watan Nuwamba.

Ana cigaba da samun karin tashin hankula gabanin zaben gwamnan da za a gudanar ranar Asabar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like