Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa karin yan Najeriya 69 aka kwaso daga kasar Lebanon a ranar Lahadi da taimakon gwamnatin kasar Lebanon.

Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama shi ne ya bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce cikin mutanen da aka dawo da su gidan akwai yan mata 50 da aka yi fataucinsu da kuma wasu matafiya 19 da suka makale a kasar.

Ministan ya mika sakon godiya ga jakadan kasar Lebanon a Najeriya, Houssam Diad da kuma Ambasada Goni Zannabura jakadan Najeriya a kasar Lebanon.