An kwaso yan Najeriya 186 daga kasar Libiya


Hukumar kula da masu yin kaura ta duniya wato IMO da kuma Tarayyar Turai EU sun kwaso karin wasu yan Najeriya 186 daga kasar Libya.

Ibrahim Farinloye, mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, a shiyar kudu maso yamma shine ya tabbatarwa da kamfanin Daillancin Labaran Najeriya NAN haka a birnin Lagos.

Farinloye ya ce mutanen sun dawo ne cikin rukuni biyu ta filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Lagos a ranakun Laraba da kuma Alhamis.

Ya ce “cikin sa’o’i 24 NEMA ta karbi yan Najeriya 186 da suka dawo daga kasar Libiya ta jirage daban-daban a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos.

Jirgi mai dauke da fasinjoji 154 ya sauka a filin jirgin saman ranar Alhamis ya yin da jirgi na biyu mai dauke da mutane 32 ya sauka a ranar Laraba.

A cewarsa mutanen da suka dawo sun hada da mata 99 maza 75, yara hudu da kuma jarirai 8.


Like it? Share with your friends!

-3
80 shares, -3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like