An kirkiro karin sabuwar masarauta a Zamfara


Majalisar dokokin jihar Zamfara ta zartar da wata doka ta kafa sabuwar masarauta da za a rika kira da Masarautar Bazai.

Hakan ya biyo bayan kudurin dokar da bangaren zartarwa ya aikewa majalisar da mataimakin shugabanta, Abubakar Gummi ya karanta a zauren majalisar dake neman a kirkiro Masarautar Bazai daga Masarautar Shinkafi.

Kudurin dokar ya kuma bukaci yan majalisar da su daga darajar Babban Hakimin Jangerru ya zuwa Sarki mai daraja ta uku da kuma sarautar Kayayen Mafara ya zuwa babban hakimi a Masarautar Talata – Mafara.

A ranar Litinin da ta gabata ne majalisar dokokin jihar ta kafa kwamitin da zai duba yiwuwar samar da masarautar ko kuma akasin haka.

Kwamitin ya gabatar da rahotonsa ranar Talata inda dokar ta tsallake karatu na biyu dana uku.

Daganan mataimakin shugaban majalisar da ya jagoranci zaman ya zartar da dokar kafa masarautar da kuma daga likkafan hakiman dake masarautun Shinkafi da Talata Mafara.

Hakan dai na nufi a yanzu jihar Zamfara mai kananan hukumomi 14 tana da masarautu 18.


Like it? Share with your friends!

-1
61 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like