An kashe yan shi’a uku a Kaduna


Kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya da aka fi sani da shi’a ta ce yan sanda sun kashe mambobinta uku yayin jerin gwano a Kaduna.

Tun da farko jami’an yan sanda sun gargadi yayan kungiyar ta shi’a da aka haramta akan gudanar da duk wani jerin gwano.

Amma yan kungiyar ta shi’a sun bijerewa gargadin inda suka shiga jerin gwano a birane daban-daban dake fadin kasarnan ta tunawa da ranar Ashura.

Sun gudanar da tattaki a birnin tarayya Abuja wanda ya gudana lafiya amma rahotannin da suke fitowa daga wasu birane ba masu dadin ji bane.

Yahaya Muhammad jami’in hulda da kafafen yada labarai na kungiyar ya bayyana cewa mutane uku aka kashe a Kaduna ciki har da karamin yaro.


Like it? Share with your friends!

-1
50 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like