An kashe yan sanda biyu yayin da ‘yan bindiga suka sace mutane bakwai a Adamawa


Yan bindiga sun kashe yan sanda biyu tare da sace mutane biyu a karamar hukumar Mubi ta kudu dake jihar Adamawa.

A tabakin, Ahmadu Dahiru shugaban karamar hukumar, lamarin yafaru ne ranar Talata akan titin Mubi-Gyela.

“Masu garkuwa da mutane suna uzzurawa al’umominmu a kullum suna sace mutane a lokutan da suka ga dama da rana tsaka da kuma dare. Sun kashe yan sanda biyu a ranar Talatar da ta wuce lokacin da suke sintiri akan hanyar Mubi-Gyela,” ya shedawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.

“Ya zuwa yanzu da nake magana da kai kwana uku da suka wuce sun sace mutane biyar a kauyen Kwaja da kuma biyu a kauyen Sauda.”

Ya ce masu garkuwar na buya ne akan tsaunukan dake kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Dahiru ya ce mutanen yankin sun yi asarar miliyoyin naira wajen biyan kudin fansa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an tura wata tawagar jami’an tsaro zuwa yankin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like