An kashe sojojin Yemen da dama a hari kan sansanin sojoji dake Marib


Hari kan sansanin sojoji na bayar da horo a kudancin Yemen ya kashe sojojin gwamnatin da dama tare da jikkata wasu akalla su 100.

Shugaban kasar Yemen ya gargadi sojoji a ranar Lahadi kan bukatar su zama cikin shirin yaki biyo bayan yadda ake cigaba da kara samun asarar rayuka masu yawa a hare-haren da ya dora alhakin kai su kan yan tawayen Houthi.

Harin ya kashe mutane 73 tare da jikkata wasu da dama wasu majiyoyin kiwon lafiya biyu suka fadawa kamfanin dillancin labarai na Rueters inda suka kara da cewa wani masallaci dake sansanin shi aka hara lokacin da mutane suka taru dan gudanar da Sallah.

Kafar yada labaran Saudiyya ta Al Hadath ta nuna wani fefan bidiyo da aka dauka biyo bayan harin da ya nuna yadda sassan mutane suka bazu a masallacin da kuma jini a darduma da kuma bango.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like