An kashe sojoji 15 a Mali


Wasu ƴan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar da ke ikirarin jihadi ne sun kashe dakaru 15 na kasar Mali.

An kai harin ne a ranar Lahadi a wani sansanin soji da ke tsakiyar yankin Segou.

Wani jami’in kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ‘yan bindigar sun isa sansanin bisa babura kuma duka wadanda aka kashe jandarmomi ne da kuma ‘yan sanda.

Masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyoyin al-Qaeda da IS na yawan kai hare-hare a Mali da kasashen da ke makwabtaka da ita.
A shekarar bara, masu ikirarin jihadin sun kashe sojoji 24 a gabashin kasar, mako daya kafin hakan an kashe jami’an tsaron kasar 54 a wani harin na daban.

A harin da aka kai a ranar Lahadi, wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da kayayyakin aiki na sojoji.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like