Mutanen da basu gaza 45 ba ne aka kashe yayin wani rikicin kabilanci a wani yanki dake fama da rikici a kasar Sudan ta kudu.

Akalla wasu 18 aka jikkata lokacin da wasu mutane dauke da muggan makamai daga kabilar Atok Buk suka kai farmaki kan wasu kauyuka da dama na yan kabilar Apuk Parek a gundumar a arewacin Tonj dake jihar Warrap a arewacin kasar.

Kwamishinan riko na lardin, Andrew Deng shi ne ya bayyana haka.

A cewar Deng kauyuka da dama aka kone kurmus yayin da dubban mutane suka tsere daga yankin.

A mahaukunta a yankin sun tabbata da cewa harin na ramuwar gayya ne kan makamancinsa da aka kai makonnin da suka wuce.