An kashe mutum guda sa’ilin da masu zanga-zanga suka kona motar yan sanda a bakin Shoprite


Wani mutum da ba a gane kowaye shi ba aka harbe har lahira a harabar kantin Shoprite dake Lekki a birnin Legas.

A cewar wani mutum da ya ganewa idonsa abinda ya faru ya bayyana mutumin da aka kashe a matsayin mai zanga-zanga kuma an kashe shi ne lokacin da masu zanga-zangar suka kunnawa motar yan sanda wuta.

Mutanen da suka fusata sun dirarwa harabar ginin shagon dake kan titin Lekki-Epe inda suke rera wakokin tayar da hankali.

Yan sandan dake jibge a wurin ne suka hanasu shiga cikin ginin kasuwar zamanin dake dauke da shagon na Shoprite hakan yasa suka shiga kona tayoyi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like