Wata tawagar jami’an yan sanda da sojoji sun samu nasarar dakile harin da yan bindiga suka kai kan kauyen Tsaskiya dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina inda aka samun rahoton mutuwar mutane shida a yayin harin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Gambo Isah ya fitar ya bayyana cewa maharan da yawansu ya kai 200 sun shiga kauyen ne ta wasu hanyoyin uku da jami’an tsaro suka saka shinge.

Ya ce maharan na dauke da muggan makamai da suka hada da bindigar AK-47, mashingan da sauransu inda suka rika harbin kan me uwa da wabi.

Ya kara da cewa bayanan sirri da suka samu ne ya basu nasarar dakile harin har ta kai sun kashe maharan biyar a musayar wutar da suka yi inda da yawa daga ciki suka tsere da raunin harbin bindiga.

Mutum na shida da ya mutu a musayar wani mahaukaci ne dake a kauyen.