An kashe mutane hudu a rikici tsakanin sojoji da jami’an tsaron kungiyar IPOB


Mutanen gari su hudu aka bada rahoton an harbe su har lahira a Orlu dake jihar Imo, biyo bayan arangamar da aka yi tsakanin jami’an soja da kuma yan kungiyar tsaro ta Eastern Security Network da kungiyar IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu ta kafa.

Rikicin ya samo asali ne bayan da aka samu sabani tsakanin sojoji da wasu matasa a yankin ranar Lahadi.

Sojojin sun mayar da martani har ta kai ga ana zargin sun kashe wani matashi kafin su bar garin.

Amma kuma daga bisani sojojin sun dawo da daddare inda suka fuskanci turjiya daga yan kungiyar ta IPOB.

Arangama tsakanin bangarorin biyu ta kai ga musayan wuta ba kakkautawa abin da ya tilastawa yan gari tserewa cikin gidajensu.

Mutane hudu ciki har da wata mace mai matsakaicin shekaru aka bada rahoton sun mutu bayan da harsashi ya kauce ya same su a musayar wutar da aka yi.

Har ila yau an kona gine-gine da dama a rikicin.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 2

You may also like