An kashe mutane 12 a harin sojan saman Afghanistan kan sansanin mayakan Taliban


Hari ta sama kan wani sansanin mayakan kungiyar Taliban dake arewa maso gabashin kasar Afghanistan ya kashe akalla farar hula 12 a cewar wasu jami’ai dake yankin.

Jerin hare-haren na dakarun sojan saman Afghanistan a yankin na arewa maso gabashin Kunduz na zuwa ne a lokacin da gwamnatin ƙasar da yan kungiyar Taliban ke gudanar da taron sulhu a kasar Qatar.

Jami’an lardin da kuma majiyar Taliban sun bayyana cewa akalla fararen hula 12 aka kashe tare da jikkata sama da mutane 10.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar ya ce an kashe mayakan Taliban sama da 40 a harin ta sama amma ba su tabbatar ba ko akwai fararen hula ko kuma babu amma suna cigaba da bincike.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like