Harin ya auku ne a kauyen Deye Koukou na yankin Banibangou, inda aka yi asarar wasu mutum 14 a ranar Lahadin da ta gabata.

Akwai ma karin wasu mutum uku da suka jikkata a sabon harin da ya faru ranar Laraba.

Jimilla dai rayukan mutane 33 ne aka rasa cikin kasa da mako guda a yankin na Banibangou.

Banibangoun ta hada iyakokin kasashen uku, wato Njar da Burkina Faso da ma kasar Mali, kasashen da duk ke fama da hare-haren masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyoyi irin su Al-Qaeda da IS na kasashen Larabawa.