AN KARRANA UWAR GIDAN GWAMNA GANDUJE DA BABBAR LAMBAR YABO TA GIRMAMAWA A JAMI’AR BAYERO


Laraba, 4 ga watan Satumba, 2019.

A ya yin wani gagarumin taron shekara da aka gudanar yau a jami’ar Bayero, (BUK) kan lamarin da ya shafi batun ingancin Ilimi a (ƙarni na 21) wato “Problems and Prospects of Accessibility to Quality Education in the 21st Century Nigeria,”

Ƙungiyar “Nigerian Association for Administration and Planning” (NAEAP), reshen Jami’ar ta (BUK) ta karrama Uwar Gidan gwamnan Jihar Kano, Hajiya, Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da babbar lambar yabo ta girmamawa dangane da tasirinta kan bunƙasa fannin Ilimi a Jihar Kano da ƙasa gaba ɗaya.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, shi ne ya miƙa lambar yabon ga uwar gidan gwamnan a harabar filin taro na jami’ar jim kaɗan da kammala karanto kaɗan daga cikin gwagwarmayar da ta yi a fannin Ilimi da kuma taimakon al’umma.

Daga ciki an bayyana cewa Uwar gidan gwamna Ganduje, Dakta Hafsat, ta yi karatunta na Al’ƙur’ani mai girma a garin Malam-Madori, kuma ta zama ɗaliba ta farko mafi ƙwazo.

A fannin karatun zamani kuwa, Dakta Hafsat, ta fara karatu a makarantar Firamare ta garin Malam-Madori, daga nan ta koma makarantar Firamare ta kwana a Shekara Jihar Kano, har ta kai zuwa Kwalejin horar da malamai mata ta Kano ta kuma je jami’ar Bayero (BUK) inda a nan ne ta kai har matakin Dakta.

Ta kuma halarci tarukan ƙarawa juna sani da dama a ciki da wajen Nageriya. Haka zalika, ta na kuma aiki da ƙungiyoyi daban-daban na ƙwararru kamar:

All Nigerian Confederation of Principals of Secondary Schools (ANCOPSS), da Nigerian Institute of Management (NIM), sai kuma Nigerian Association of Educational Administration and Planning (NAEAP), da sauransu da dama.

A fannin aikin koyarwa ma, Dakta Hafsat, ta taɓa riƙe muƙamai da dama, misali ta taɓa zama: head of department, senior Mistress, Vice Principal, Principal, Inspector of Education and Deputy Director in Secondary Education Board a birnin tarayya Abuja.

A fannin ayyukan jinƙai kuwa, Dakta Hafsat Ganduje, ta na aiki da gidauniyar (Ganduje Foundations), inda su ke aikin taimakon marasa lafiya da sauran ayyukan jinƙai. Sannan kuma ta na ba da gudunmawa wajen tallafawa mata da jarin sana’o’i.

Ta fannin Iyali kuwa, sun bayyana cewa Dakta Hafsat Ganduje ta na da ƴaƴa kimanin bakwai waɗanda kuma dukkanninsu masana ne a fannoni daban-daban na Ilimi. Ta na kuma da jikoki.

Da ta ke maida jawabi, uwar Gida, Hajiya Dakta Hafsat Ganduje, ta bayyana jindaɗinta a madadin iyali gaba ɗaya kan wannan karramawa da ƙungiyar ta yi mata.

Shi ma a nasa jawabin, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana karramawar a matsayin abin farin ciki, wacce kuma za ta taimaka wajen ƙara musu ƙarfin gwiwa gaba ɗaya.


Like it? Share with your friends!

1
105 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like