An samu karin mutum guda da ya kamu da Coronavirus a Bauchi.


Hukumomi a jihar Bauchi sun tabbatar da samun mutum na biyu da ya kamu da cutar Coronavirus.

Kwamishinan lafiya na jihar,Aliyu Maigoro shine ya sanar da haka ranar Alhamis.

Da yakewa yan jaridu karin bayani kan halin da ake ciki game da cutar a jihar, kwamishinan ya ce cikin mutane 48 da aka gwada an samu mutum guda yana dauke da cutar.

Idan za a iya tunawa gwamnan jihar ta Bauchi, Bala Muhammad ya kamu da cutar Coronavirus abin da ya jawo fargabar ya yadawa wasu na kusa da shi.

Kwamishinan ya ce wani mutum mai shekaru 62 shine mutum na biyu da ya kamu da cutar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like