An Kammala Tantance ‘Ya’yan Talakawa Guda 700 Da Gwamnan Yobe Zai Dauki Nauyin Karatunsu Zuwa Kasashen Waje


Kwamiti tantancewa na musamman karkashin jagorancin, Dr. Sharif Muajirin, ta kammala jarrabawar tantance ‘yan takarar neman tafiya karin Karatu a kasashen waje wanda tsarin (Mai Mala Buni International Schoolership Award) ya shirya daukar nauyin tura yaran talakawa guda 700 a manyan kashen Duniya domin samun nagartaccen ilimi a bangare daban-daban.

Kimanin yaran talakawa guda 2,116 ne suke rubuta jarrabawar tafiya (Masters da PhD), sai yaran talakawa 4,121 wanda suka rubuta jarrabawar tafiya jami’ar farko, a babbar birnin jihar Yobe, Damaturu.

Domin tabbatar da adalci ga wanda sukaci jarrabawar, tsarin jarrabawar tantance yan takarar neman tafiya karin Karatu, ya kasance a na’ura mai kwakwalwa ne, ta yadda zai tantance su ba tare da nuna sanayya ko wariya ba, wanda suka samu maki da cika ka’idane kawai zasu samu wannan garaɓasa ta Mai girma Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni.

Shugaban kwamitin Dr. Sharif Muajirin, ya damka rahoton kammala tantancewar ga Gwamna Mai Mala Buni.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like