An kammala ceto mutanen dake ƙarƙashin ginin benen da ya rufta a Lagos


Adesina Tiamiyu, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos, LASEMA ya ce ya zuwa yanzu babu wani mutum da ya rage cikin baraguzan ginin bene mai hawa uku da ya ruguzo a yankin Ita Faji dake jihar.

Tiamiyu ya bayyana haka lokacin da yake magana da yan jaridu a wurin da lamarin yafaru.

“Mun dakatar da aiki da misalin karfe uku na dare bayan da muka zakulo gawar wani mutum, mun tabbata cewa babu wanda yayi saura karkarshin baraguzan ginin,” ya ce.

Amma wasu mazauna yankin sun musalta ikirarin na shugaban hukumar ta LASEMA inda suka dage kan cewa har yanzu akwai sauran mutane da suka rage a karkashin baraguzan ginin.

Ginin benen mai hawa uku dake ɗauke da makarantar firamare a hawa na biyu ya rufta ranar Laraba da safe lokacin da dalibai suke tsaka da karatu cikin ajinsu.

Akalla mutane 12 ciki har da yara tara aka tabbatar da mutuwarsu.


Like it? Share with your friends!

-1
92 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like