An kama yan Najeriya 33 a Kenya


Ƴansanda a kasar Kenya sun kama wasu yan Najeriya 33 da ake zargi da zama cikin kasar ba tare da izini ba.

An kama mutanen ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Kasanrani dake babban birnin kasar Nairobi bayan da aka rawaito suna zaune unguwar tun bayan da suka iso a lokuta mabanbanta.

Da yake magana da yan jaridu, Peter Kimani jami’in dansanda dake kula da yankin Kasanrani ya ce jami’an rundunar dake yaki da miyagun kwayoyi sune suka kama mutanen bayan da suka samu bayanan sirri dake nuna cewa an mayar da yankin wani da dandali da ake tura miyagun kwayoyi sassa na duniya daban-daban.

Ya ce har ila yau an kama wani mutum dan kasar,Eriteria da shima ake zarginsa.

Kimani ya ce mutanen da ake zargi sun fake da cewa su daliban jami’a ne inda suke gudanar da kasuwanci da zummar fara sayar da miyagun kwayoyi.

Tuni dai bayan gurfanar dasu gaban kotu hukumomin kasar suka fara shirya takardun taso keyarsu gida.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like