An Kama ‘Yan Kasuwar Da Suka Sayar Da Abin Sha Mai Guba A Kano.Mutane 3 ne ake hasashen sun mutu sanadiyyar shan wasu nau’o’i na abin sha a jihar Kano a cikin watan Maris, wadanda binciken farko ya nuna suna kunshe da sinadirai masu guba da lahani ga lafiyar dan adam.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Olusayo Akintola ya fitar, ta ce hukumar ta sami nasarar kama ‘yan kasuwar da ke da hannu a sayar da kayayyakin, duk da yake dai ba’a bayyana sunaye ko adadin mutanen da aka kama ba.

Farfesa Mojisola Adeyeye, Shugabar Hukumar NAFDAC

Farfesa Mojisola Adeyeye, Shugabar Hukumar NAFDAC

Sanarwar ta ce shugabar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta yi gargadi akan yin karin sinadirai ga abinci da ababen sha domin karin dandano, tana mai cewa hakan kan iya haifar da mummunan rashin lafiya da kuma mutuwa.

Adeyeye ta ce “hukumar ba za ta yi saku-saku ba, wajen tabbatar da inganci da sahihancin abinci da magunguna da ake sayarwa jama’a a kasuwanni.”

Ta ce tuni da hukumar ta aike da sakamakon binciken farko da ta yi akan wadanda lamarin ya rutsa da su a Kano, zuwa ga gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin ziyarar da ta kai ta kwana 2 a jihar sakamakon al’amarin.

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Ta ce babbar nasara ce da aka sami kama ‘yan kasuwar da suka kawo abin shan mai dauke munanan sidadirai, wanda hakan zai ba da damar fadada bincike da daukar matakan da suka dace.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.