An kama yan fashin banki a Abuja


Da safiyar ranar Asabar ne wasu yan fashi suka kai hari wani bankin kasuwanci dake unguwar Mpape a wjawny birnin tarayya Abuja.

Da isarsu bankin sun shiga harbin kan me uwa da wabi kafin daga bisani su kutsa kai ciki.

Shigar suke da wuya jami’an yan sanda da na sojoji suka iso wajen inda suka yiwa bankin kawanya.

Bayan da aka dauki tsawon lokaci a karshe jami’an tsaron sun samu nasarar kashe daya daga cikin yan fashin lokacin da ya yi kokarin tserewa tare da kama hudu daga cikin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like