Jami’an hukumar kula da shige da fice ta Naiejriya (NIS) sun kama wasu ‘yan asalin kasar Nijar su biyu da kananan bindigogi, Kwamfutoci da wayoyin hannu a kan iyakar kasar nan da ke Kongolam, ta shiyyar Katsina.

Jami’in yada labarai na hukumar ta NIS, Mista Sunday James, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

A cewar sa, an samu nasarar kama mutanan ne a sakamakon hanzarta aikin da jami’an hukumar ta NIS suka yi a kan iyakan.

“Wannan namijin kokarin da Jami’an hukumar suka yi ya biyo bayan ziyarar da babban Kwanturolan hukumar ta shigi da fici, Muhammad Bababndede da kuma takwaransa na hukumar Kwastan Kanar Hameed Ali mai ritaya suka kai ne domin duba yanayin hadin kan da ake samu na yin aiki a tare da kuma nasarorin da aka samu.

James ya kara da cewa, ‘yan Nijar din guda biyu sun budewa jami’an hukumar wuta a kokarin da suka yi na neman hanyar tserewa kamun su.

Zaratan jami’an namu sun ci karfin su, inda suka yi nasarar harbe gudansu har lahira, sa’ilin da gudan da suka kama yake bayar da bayanai masu mahimmanci.

“Bayan an kare yi masu dukkanin tambayoyi da daukan bayanan su, za a hannanta wanda aka Kaman cikin su ga rundunar ‘yan sanda domin ci gaba da daukan matakan da suka dace.”

Ya shawarci al’ummun da suke a kan iyakokin da su guji hada kai da batagari da nufin yi wa kokarin da gwamnati ke yi kafar Ungulu, domin tabbatar da tsaron kan iyakokin namu.