An kama wasu mutane da naira miliyan 3.7 na jabu


Rundunar yan sandan jihar Plateau ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da mallakar kudin jabu da yawansu ya kai naira miliyan uku da dubu dari bakwai.

Kudin jabun sun hada da bandir yan naira ₦1000 guda 30 da kuma rabin bandir na yan ₦1000 guda 14.

Kwamishinan yan sandan jihar,Isaac Akinmoyede da yake nuna mutanen ga manema labarai ranar Juma’a, ya ce Isa Ibrahim dan asalin Mayo-Belwa ta jihar Adamawa da kuma wani Danjuma Yilbis daga Ron a karamar hukumar Bokkos ta jihar Plataeu an kama su da laifin mallakar kudin bogi ranar 30 ga watan Agusta biyo bayan samun bayanan sirri.

Har ila yau kwamishinan ya yi holin wasu mutane 10 da ake zarginsu da hada baki wajen kashe wani mutum Nden Gungnim na kauyen Gur a karamar hukumar Langtang ta arewa.


Like it? Share with your friends!

-4
65 shares, -4 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like