An kama Wani Mutum Mai Safarar Mutane Zuwa Kasashen Turai  A Jihar Edo Hukumar yaki da fataucin mutane ta kasa NAPTIP, ofishin shiya dake  Benin  sun kama wani mutum dan shekara 33 ,mai suna Monday Ugbo, da laifin safarar mutane.

An kama mutumin bayan da jami’an hukumar suka shafe makonni suna bibiyarsa. 
A wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar,Josia Emerole, ya fitar tace an samu nasarar ceto mutane uku daga gidansa mai namba 72 layin Osayande cikin garin Benin a jihar Edo. 

Sanarwar tace “jami’an hukumar sun dade suna bibiyarsa na tsawon makonni,bayan da ake yawan anbaton sunansa a laifuka da yawa da suka shafi fataucin mutane a shiyar da hukumar ta samu ”

“Bayan samun bayanan sirri cewa yana boye da wasu mata  a yunkurin da yake na fataucinsu zuwa kasashen waje, jami’an hukumar sun cimmasa a safiyar ranar juma’a suka kamashi a lokacin da yake karbar naira 50,000 daga cikinsu domin yimusu rijista” 

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa yana shirin daukar matan zuwa wani kogi domin suyi rantsuwa kafin su dauki hanyar tafiya zuwa kasashen Turai. 

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa Ugbo ya dade acikin gudanar da harkar safarar mutane inda yake fakewa da cewa shi magini ne. 

Comments 0

Your email address will not be published.

An kama Wani Mutum Mai Safarar Mutane Zuwa Kasashen Turai  A Jihar Edo 

log in

reset password

Back to
log in