An kama wani mutum da ya yi luwadi da yara 10


Hukumar NAPTIP dake yaki da fataucin mutane ta kama wani dan aiki, Usman Abubakar mai shekaru 21 da ake zargi da yin luwadi da yara 10 a Sokoto.

Kwamanda shiya na ofishin hukumar dake Sokoto,Hassan Tahir wanda ya bayyana haka ga manema labarai ya ce dukkanin yaran ‘yayan mutumin da ya ke wa aiki ne.

A cewar Abdullahi mutumin da ake zargi ya amsa laifin yin luwadi da yaran su 10 a yankin Rungumi dake karamar hukumar Sokoto ta kudu.

A cewarsa Abubakar ya kasance alamajiri kafin a dauke shi a matsayin dan aiki shekaru 10 da suka wuce.

Ya ce mutumin da ake zargi wanda dan asalin jihar Kebbi ne za a gurfanar da shi gaban kotu nan bada jimawa.

Da yake magana da manema labarai Abubakar ya ce wani mazaunin yankin mai suna, Malam Muntari shine ya jefa shi cikin dabi’ar luwadi lokacin yana da shekaru biyar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like