An kama wani malami yana lalata ta dubura da dalibarsa mai shekaru biyar a cikin masallaci


Jami’an ƴansanda a jihar Lagos sun kama wani mutum mai shekaru 43 da ake zargin da yin lalata ta dubura da wata yarinya yar shekara 5.

Ƴansanda sunce an kama Abdulsalam Salaudeen, bayan da aka ɗauki hoton bidiyonsa yana aikata laifin da yarinyar da yakamata ace yana koyawa karatun larabci.

Salaudeen ya shafe lokaci mai tsawo yana aikata haka sai dai dubunsa ta cika bayan da wani makoci da abin yake damunsa ya dauki hoton bidiyonsa.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Lagos Chike Oti wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce a ranar Juma’a 28 ga watan Disamba ne wani dan kasa nagari yaje hedkwatar rundunar da fefan bidiyon inda ya nemi ganin kwamishinan ƴansandan jihar.

Oti ya ce bayan da kwamishinan ya kalli bidiyon ne ya bawa jami’an binciken asiri na rundunar damar zuwa su kama malamin.


Like it? Share with your friends!

4
113 shares, 4 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like