An kama wani mai safarar sassan jikin bil’adama a jihar Niger


Wani mutum da ake zargi da safarar sassan jikin bil’adama ya fada hannun jami’an tsaro a jihar Niger bayan da aka same shi da mallakar kwayar idon mutum.

Shu’aibu Ibrahim, mai shekaru 35 wanda dan asalin kauyen Safiu ne dake karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa an rawaito ya fada hannun jami’an ƴansanda masu bincike dake aiki a ofishin ƴansanda na Gawu Babangida dake karamar hukumar Gurara lokacin da suke gudanar da sinitiri.

Ƴansanda sun ce kwayar idon an ciro ta ne daga jikin wata gawa da aka kashe a fadan kabilanci tsakanin al’ummomin Bassa da Igbira a jihar Nasarawa.

Jami’an ƴansandan sun ce mutumin ya shafe shekaru biyar yana safarar sassan jikin bil’adama kafin ya fada hannun jami’an tsaro.

Wani abokin ta’adarsa mai suna Ojo wanda zakara ya bashi sa’a shine ya bashi idon ya sayar kan kudi ₦250,000.

Mutumin da ake zargi ya tabbatarwa da yan jaridu cewa shi dan aike ne tsakanin Ojo da kuma masu saya.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like