An kama wani jirgin ruwa dauke da makamai a Afrika ta Kudu akan hanyarsa ta zuwa Lagos


Hukumomi a kasar Afrika ta Kudu sun tsare wani jirgin ruwa na kasar Russia wanda ke dauke da makamai akan hanyarsa ta zuwa Najeriya.

Hukumomi sun gano bama-bamai a cikin jirgin ruwan lokacin da suke tsaka da gudanar da aikinsu a tashar jirgin ruwan Ngqura dake wajen gabar ruwan tashar Elizabeth.

Haramtattun kayan na kan hanyarsu ta zuwa Najeriya da kuma kasar Amurka.

Abubuwan fashewar da kuma makaman da kudinsu ya kai miliyan 50 na kudin ƙasar an gano su ne biyo bayan tseguntawa jami’an da aka akayi, bayan da jirgin ya sauke wasu kwantenoni 14 a tashar.


Like it? Share with your friends!

-1
104 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like