An Kama Wani Fasto Yana Sayar Da Tikitin Aljannah


Jami’an tsaro a kasar Zimbabwe sun kama wani mai wa’azin Kirista tare da matarsa, bisa zargin sayar da tikitin Aljanna.

Pastor Tito Wats ya shaidawa dubban magoya bayansa cewa Yeso ya bayyana gare shi tare da bashi tikitin shiga Aljanna don a bai wa masu zunubi su samu damar shiga Aljanna.

Ya ce, “Ban damu da abin da mutane ko ‘yan sanda suke fada ba game da ni, ana zalunta ta ne kawai saboda aikin Allah da nake yi.”

“Yeso ya bayyana min kuma ya bani tikiti da aka yi su da danyen zinare, domin in sayar ga masu neman ceto,” a cewar wannan Pastor.

Dubban jama’a magoya bayan wannan malamin Kirista ne suka yi zanga zanga suna masu kira ga ‘yan sanda su sake shi ba da bata lokaci ba, domin kuwa kudinsu ne suke amfani da shi wajen sayen ceto.


Like it? Share with your friends!

-4
67 shares, -4 points

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Man yahdiyallahu fahuwa muhtaddi
    Waman yudilill falahadiyalahu
    Allahumma had in I ilasiradallmustakim
    Allah yakiyaye Yakima tsaremu DA kafurci
    Ameen

You may also like