An kama wadanda suka ci naman dan sanda a lokacin zanga-zangar EndSARS


Jami’an yan sanda a jihar Oyo sun samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da cin konannen naman gawar wani jami’in dan sanda a jihar.

Mutanen sun aikata laifin a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar EndSARS.

Daya daga cikin mutanen da aka kama an same shi ne da laifin dauke kokon kan marigayin.

A wani fefan bidiyo da aka wallafa a kafafen sadarwar zamani a lokacin zanga-zangar ya nuna yadda matar ta ciri ya’yan marainan jami’in dan sandan kana ta saka a baki.

Sai dai bayan da ta faɗa komar jami’an tsaro matar ta musalta cin ya’yan marainan inda ta ce kawai ta dauke su ne inda ta mikawa wani.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Thank you for this very good posts. I was wanting to know whether you
    were planning of publishing similar posts to this.
    Keep up writing superb content articles!

You may also like