An Kama Na Hannun Daman Buhari Da Fasfo Na Bogi Da Kuma Yunkurin Shiga Da Kudade Kasar Waje


Jami’an tsaro a kasashen Turai, sun kama Nasiru Danu, mai kula da duk wasu al’amurran shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An kama Nasir Danu ne a filin sauka da tashin jiragen sama na ‘Heathrow’ dake kasar Turai, bisa zargin sa da amfani da fasfo na bogi da kuma zargin fitar da makudan kudade daga Nijeriya zuwa kasar Turai.

A gefe daya kuma, a wata takarda da jam’iyyar PDP ta fitar, ta ofishin babban sakataren jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan, PDP ta ce shirun da fadar shugaban kasa ta yi tun bayan faruwar lamarin ya nuna fadar shugaban kasa ta yarda da faruwar laifin wanda makusancin shugaba Buhari ya aikata.

“Wannan kuma ya kara tabbatar da kama Nasir Danu da aka yi a bainal-jama’a bisa zargin sa da fitar da makudan kudin sata da ake zargin mallakin wani makusanci ne ga fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar PDP ta ce dole ne fadar shugaban kasa ta fito ta yi magana kan wannan abin kunya da ake zargin Nasir Danu ya dade yana aikatawa na fitar da makudan kudade da aka ce yana da alaka da shugaban kasa da wasu ‘yan kwangilar Mai wanda ake fitar da Biliyoyin nairori daga Nijeriya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like