An kama mutane uku da sassan jikin bil’adama a Nasarawa


Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa ta kama wasu mutane uku da take zargi da laifin mallakar sassan jikin bil’adama.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar,Kennedy Idirisu shine ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya haka ranar Litinin a Lafia babban birnin jihar.

Idirisu ya ce sojojin Najeriya dake gudanar da aiki na musamman ne suka kama mutane inda suka damka su hannun ƴansanda.

A cewarsa mutanen da ake zargi ranar 1 ga watan Nuwamba sun hako wata sabuwar gawa a wata makabarta dake Mararaban-Akunza inda suka cire mata hannu kana suka mayar suka binne.

Mazauna yankin sun samu labarin faruwar lamarin kuma suna dab da kona mutanen ne sojoji suka isa wurin inda suka ceto su kuma suka mika su hannun ƴansanda.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like