An kama masu fasa kwauri su 9 a Katsina


Mutane 9 ne suka fada hannun jami’an hukumar kwastam a Katsina bayan da aka zarge su da yunkurin fasa kwaurin kayayyaki iri daban-daban da aka haramta shigowa da su cikin kasarnan.

Kwantirolan a hukumar dake kula da jihohin Kaduna da Katsina, Abdullahi Kirawa shine ya bayyana haka lokacin da yake holin wasu daga cikin kayayyakin da aka samu a wurin masu fasa kwaurin inda ya ce harajin kudin kayan ya kai miliyan ₦62.

Ya yi kira ga mutane da su taimakawa hukumar kwastam da sahihan bayanai da za sukai ga dakile ayyukan masu fasa kwauri dake neman nakasa tattalin arzikin kasa.

Ya lissafa kayan da suka kwato da suka hada da buhunan shinkafa 1,367, galon din manfetur 295, dilar gwanjon kaya 297, turamen zani 75, jarkokin mai guda 295 mai cin lita 25, buhunan suga dan waje guda 53, katon din batiri 14, baburan hawa 15 da kuma motoci biyar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like