An kama manomin tabar wiwi a jihar Kwara


Hukumar NDLEA mai yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta ce ta gano wata gona a Ilorin babban birnin jihar Kwara da ake noma ganyen tabar wiwi.

Bayanin gano gonar ya fito ne lokacin da hukumar ta nunawa manema labarai manomin mai suna, Nasiru Salisu da kuma wata motar tirela da aka kama tare da mutanen cikinta su 5 akan hanyar Jebba-Mokwa dauke da ganyen tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 500.

Da yake holin mutanen kwamandan,NDLEA a jihar Kwara, Ambrose Umoru ya ce sun kama manomin ne a yankin Kulende, Sango dake Ilorin ya yin da suka kama motar tirelar biyo bayan samun bayanan sirri da suka samu daga wasu masu samar musu da bayanai.


Like it? Share with your friends!

1
59 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like