An kama manomin ganyen tabar wiwi a jihar Kebbi


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA ta kama wani magidanci mai yaya shida, Abdullahi Sani bisa laifin shuka ganyen tabar wiwi a gonarsa dake kauyen Shingi a karamar hukumar Danko/Wasagu.

Kwamandan hukumar a jihar, Peter Odaudu lokacin da yakewa yan jaridu bayani ranar Juma’a ya ce gonar ganyen tabar wiwin itace ta biyu mafi girma da aka taba samu a jihar.

Ya ce “Bayan samun rahoton bayanan sirri tawagar jami’an NDLEA a jihar ranar 5 ga watan Satumba,2019 sun gano tare da lalata gonar tabar wiwi a kauyen Shingi.”

Sama da kilogiram 46 na ganyen tabar jami’an suka tsige a gonar.

Ya kara da cewa mutumin da ake zargi da mallakar gonar yana tsare a hannunsu.

Da yake amsa tambayoyin yan jarida mutumin da ake zargi ya ce ya shuka ganyen tabar ne domin bukatar kansa da kuma abokansa dake bukatar sha.


Like it? Share with your friends!

-1
63 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like