An Kama Kasurgumin Dan Ta’addan Dake Haddasa Rikicin Garin Kasuwar Magani A Kaduna


Babban dan ta’addan nan da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan al’umma masu dimbin yawa a yankin Kasuwar Magani dake jihar Kaduna, mai suna Joshua Zidane da hukumomin tsaro ke nema ruwa-a jallo yau dinnan ya shiga hannu.

Rahotan da muke samu ba da jimawa ba, ya nuna daga lokacin da aka cafke shi a jiya har wasu jama’ar yankin nasu marasa son zaman lafiya sun fara tare hanya suna dukan mutane. Wanda da fara hakan Gwamna Malam Nasir ElRufai ya baiwa jami’an tsaro umarni inda nan da nan ba suyi ƙasa a guiwa ba suka bazama cikin gari da kewaye inda suka samar da tsaro tare da tabbatar da bin doka da oda.


Like it? Share with your friends!

2
104 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like