An kama Barayin Da Suka Addabi Mutane Akan Hanyar kaduna Zuwa Abuja 


An kama wasu rikakkun yan fashi su shida da suka addabi matafiya akan hanyar kaduna zuwa Abuja. 

Rundunar tsaro ta musamman a jihar da ake kira da Operation Yaki ta bayyana wannan gagarumar nasara da aka samu yau lahadi a garin Kaduna. 

An kama mutanen a ranakun Alhamis da juma’a, bayan da jami’an tsaro suka dade suna bibiyarsu. 

 Samuel Aruwan mai magana da yawun  gwamnan jihar yace an kama mutanen ne biyo bayan jibge jami’an yan sanda da kuma kara yawan motocin jami’an tsaro dake sintiri a yankin. 

” wannan kokarin ya haifar da kama masu laifin ciki har da shugabansu Adamu Mamman mai shekaru 35, da yafito daga kauyen Amana a karamar hukumar Igabi, Ali Rabo da akafi sani da Blaky na kauyen Liman Ibada, a karamar hukumar Chikun, Auwalu Ahmad da akafi sani da Mota,  wanda ya fito daga kauyen Rijana  a karamar hukumar Kachia, wanda shine babban mai sanar dasu bayanai akan hanyar kaduna zuwa Abuja. 

  ” sauran wadanda aka kama sun hada da Shehu Idris Shagari mai shekara 27, na kauyen Gadan Gayan  a karamar hukumar Igabi, Umar Antijo daga kauyen Rijana da kuma Babangida Abdullahi wanda shine mai karbar wayar hannu da kuma na’urar mai kwakwalwa ta tafi dagidanka da ake kira laptop. 
 Da yake sanar da kama mutanen, jami’in tsare-tsare na Operation Yaki, Yakubu Yusuf,yace,gwamnati jihar kaduna ce take daukar nauyin shirin.

An kama masu laifin a wurare daban-daban da suka hada da Mararrabar Jos,  unguwan Pam, kauyen Rijana duk a jihar Kaduna. 

Dukkan wadanda aka kama sun bayyana yadda suka sace matafiya da dama akan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja. 

Tuni dai aka mika su ga sashin binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan jihar. 
  

Comments 0

Your email address will not be published.

An kama Barayin Da Suka Addabi Mutane Akan Hanyar kaduna Zuwa Abuja 

log in

reset password

Back to
log in