An kama ƴansanda biyar da suka kashe wata mace a jihar Lagos


Rundunar yansandan jihar Lagos,ta kama tare da tsare wasu jami’anta biyar da ake zargi da kashe wata mata a unguwar Ajegunle dake jihar.

Mai magana da yawun rundunar,DSP Bala Elkana cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce lamarin yafaru ne a layin a layin Amusa a unguwar ta Ajegunle.

An kuma zargin ƴansandan da harbe Emmanuel Akomafuwa, mai shekaru 32 mazaunin layin Babatunde dake olodi Apapa.

“An garzaya da mutanen asibitin inda aka tabbatar da mutuwar Ada Ifeanyi ya yin da Emmanuel Akomafuwa yanzu yake kwance a asibiti inda yake samun kulawa sakamakon raunin da ya samu sanadiyyar harbin.

“Mambobin tawagar jami’an tsaron da ake zargin suna da hannu a harbin da suka fito daga caji ofis na Trinity na can na fuskantar hukunci a hedkwatar rundunar dake Ikeja,” ya ce.


Like it? Share with your friends!

1
80 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like