A cewar masu aiko wa kamfanin dillancin labaran AFP sun ce maharan guda biyu daya dauke da wuka sun farwa shugaban ne a harabar masallacin Idi, kuma nan take jami’an tsaro suka gudu da shi, sai dai babu tabbacin ko ya samu rani ko a a.

Dama kasar Mali na fama da tarzoma na mayakan jihadi tun a shekarar 2012, matsalar da ta yadu zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar ga kuma rikicin siyasa a gefe guda da ya jefa kasar cikin rashin tabbas.