An kai hari ofishin MTN a Abuja tare da kona tayoyi a bakin Shoprite


Wasu gungun matasa dake da adawa da zanga-zangar kin jinin baki dake gudana a kasar Afrika ta Kudu sun lalata wasu kayayyaki a ofishin MTN dake Karu kusa da babban birnin tarayya Abuja.

Har ila an samu ya mutsi a Shoprite dake Lugbe akan titin zuwa filin jirgin sama na Abuja lokacin da yan sanda suka rika harba hayaki mai sa hawaye a kokarin da suke na dakatar da wasu bata gari daga kona babban shagon sayar da kayayyaki.

Jami’an yan sandan kwantar da tarzoma sune suka dakatar da masu zanga-zangar dake son kona shagon na Shoprite.

Amma sun rika kona tayoyi akan hanyar dake kusa da shago kana suka dage kan cewa baza su tafi ba har sai sun aiwatar da nufinsu.

An dai samu kai hare-haren ramuwar gayya kan kamfanoni dake da alaka da kasar Afirka ta Kudu tun bayan da aka fara zanga-zangar kin jini baki kasar.

An kona shaguna da dama na yan kasashen Afrika mazauna kasar Afrika ta Kudu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like