An kafa kwamitin da zai gano wadanda suka kashe yan sanda 7 a Abuja


Ibrahim Idris, babban sifetan yan sandan Najeriya ya kafa wani kwamiti mai mutane 8 da zai binciki musabbabin kisan wasu jami’an ‘yan sanda bakwai a birnin tarayya Abuja.

Wasu yan bindiga ne da ba’asan ko suwaye ba suka kashe yan sandan a wani shingen binciken ababen hawa dake yankin Galadimawa a birnin tarayya Abuja.

Jimo Moshood, mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa kwamitin ya kunshi kwararrun masu binciken laifuka.

Kwamitin zai kasance a ƙarƙashin kwamishinan yan sanda, Bala Chiroma wanda kwararre ne wajen bankado masu aikata laifuka.

Moshood ya kara da cewa kwamitin zai kammala aikin da aka bashi cikin kwanaki 21.


Like it? Share with your friends!

-1
108 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Allah ubangiji ya taimaka ya kuma bada sa’a ya kuma baku ikonyin Adalci acikin wannan aiki naku

You may also like