An kaddamar da shugabannin R-PDP a Adamawa


An kaddamar da shugabannin tsagin jam’iyar PDP a jihar Adamawa da ake kira R-PDP.

R-PDPn ta dauki wannan matakin ne duk da yunkurin da jami’an tsaro suka yi na hana su isa inda suka shirya gudanar da taron nasu a otal din Lalewal dake Jimeta. Hakan ya tilasta musu taruwa a gidan jagoransu wato, Dr Umar Ardo.

Tsagin na jam’iyar PDP sun dade basa ga maciji da yan jam’iyyar PDP tun lokacin da suka sanar da kafa tsagin nasu shekarar da ta wuce mako biyu da suka wuce ne wasu yan daba suka tarwatsa inda suke taro har ta kai sun raunata mutane uku.

Ardo da magoya bayansa sun dade suna kokawa kan yadda ake gudanar da jam’iyar PDP a jihar.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like