An jibge tarin sojoji na musamman a ginin majalisar dokokin Amurka


Biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a birnin Washington na ƙasar Amurika da ta kai ga mamaye ginin harabar majalisar dokokin kasar.

A yanzu haka an jibge tarin sojoji na musamman domin tsaron ginin majalisar gabanin rantsar da sabon shugaban kasar, Joe Biden.

Magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Donald Trump ne suka mamaye ginin domin nuna adawarsu da tabbatar da zaben Joe Biden da majalisar ta shirya gudanarwa


Like it? Share with your friends!

0

You may also like