An jibge jami’an tsaro gabanin zaben gwamnan Ondo


Kasa da sa’o’i 24 suka rage kafin masu kada kuri’a su fita zuwa tashoshin zabe a jihar Ondo an jibge jami’an tsaro masu yawa dake gudanar da sintiri a Akure babban birnin jihar da kuma wasu garuruwa.

Mutane da dama sun ga jerin ayarin gamayyar jami’an tsaron da suka hada da sojoji, yan sanda, jami’an Civil Defence suna gudanar da sintiri na hadin gwiwa.

Ana dai fargabar samun rikici a zaben na ranar Asabar duba da yadda aka rika samun tashin hankali a lokacin da yan takarkarun ke gudanar da yakin neman zabe.

Ana ganin zaben na ranar Asabar karawa ne a tsakanin yan takara uku duk da cewa akwai sauran yan takara da suke wasu jam’iyu na daban.

Manyan yan takara a zaɓen sun hada da dan takarar jam’iyar APC kuma gwamna mai ci,Rotimi Akeredulu, sai Eyitayo Jegede na jam’iyar adawa ta PDP sai kuma Ajayi Agboola na jam’iyar ZLP wanda shi ne ke rike da mukamin mataimakin gwamnan jihar.

Leave your vote

Comments are closed.

6,582 Comments

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg