Majalisar sojin da ke mulki a kasar Chadi a wannan Lahadin, ta bayar da sanarwar dage dokar hana zurga-zurgar da suka kakaba, sa’oi kalilan bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Idris Deby Itno.

Dokar dai ta fara aiki tun a ranar 20 ga watan Apirilun da ya gabata, inda aka kwashe kusan makwanni biyu ke nan ba shiga ba fita a kasar daga karfe 6 na yamma zuwa 5 na asuba kamin daga bisani a sassafta ta daga 8 na yamma.

Mai magana da yawun majalisar sojin  Azem Bermandoa Agouna ya ce matakin  janye dokar ya biyo bayan samun saukin al’amuran tsaro da aka yi a ciki da iyakokin kasar.