An harbe matafiya biyu a Filato


Mutane biyu yan bindiga suka harbe har lahira ranar Lahadi a kauyukan Fanlo da Nding dake karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.

Terna Tyopev mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar shine ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin.

Ya ce mutanen da abin ya shafa suna tsaka da tafiya aka kai musu hari. Ya kara da cewa mutane biyar ne suka samu raunuka daban-daban a harin.

“Jiya da karfe 8 na dare caji ofis namu dake Barkin Ladi ya samu kiran kai daukin gaggawa dake cewa wasu yan bindiga da ba’asan su waye ba sun kai wa wata mota kirar Pueguot 504 mai rijista AA 393 TSF hari,”Tyopev ya ce.

“Mai kiran ya ce mutanen na kan hanyarsu ta zuwa kauyen Nding daga Fanlo lokacin da aka kai musu harin.

“Lamarin ya jawo mutuwar wani mai suna Samuel Stephen mai shekaru 28 da kuma Dajugu Randong mai shekaru 28.

Mai magana da yawun rundunar ya ce jami’ansu sun isa wurin da abin ya faru kuma suna cigaba da kokarin kama wadanda suka kai harin.


Like it? Share with your friends!

1
48 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like