An harbe dan sanda a wani shingen bincike


Wasu yan bindiga sun harbe wani dan sanda da ake kira Lasisi mai mukamin Insifecta a wani shingen bincike dake kan hanyar Isua-Ise Akoko ta jihar Ondo.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun fito ne daga cikin daji inda suka budewa marigayin wuta tare da abokanan aikinsa dake aiki da ofishin yan sanda na Isua Akoko.

“Yan sandan sun shafe fiye da shekara daya suna aiki a shingen binciken. Yau wasu batagari kawai sun fito daga inda ba a sani ba sun bude musu wuta .Ya yin da aka kashe Lasisi nan take sauran abokan aikinsa sun ranta a nakare,” a cewar wata majiya dake wurin.

“Bayan an kashe shi batagarin sun tafi da bindigarsa.”

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like